<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><title>Mai Cetonmu Zai Zo, Misalin Walƙiya LW121</title>
<lyrics>[V1]
 1) Mai Cetonmu zai zo, misalin walƙiya,
 Da ƙafon Allahnmu, lalle zai sake zuwa.
 Da kiransa mai ƙarfi kuwa,
 Da ikonsa zai sake zuwa.

[V2]
 2) Ga zancen ranan nan, tana ta zuwansa,
 Ku yi ta tsaronku, ku yi ta jiransa.
 Ku yi biyayya dukanku,
 Ku adalai, yi shirinku.

[V3]
 3) Mai Cetonmu zai zo, zai amshi mulkinsa,
 Numfashin bakinsa zai ci maƙiyansa.
 Zai ƃaƃƃata magautansa,
 Zai cinye su da ikonsa.

[V4]
 4) Ya Ubangiji zo, Ango Ekklesiya
 Ka zo da cetonka, ka gama alkinka
 Ka ji add'o'inmu yau,
 Ka zo, ya Ubangiji, zo.</lyrics>
<hymn_number>121</hymn_number>
</song>